Mutane da dama a Amurka dake kalubalantar shugaban kasa Donald Trump sunce ya kamata ya bayyana takardun sa na haraji a fili kamar yadda kowanne shugaban kasar Amurka yayi fiye da shekaru Arba’ain a baya.
Mutane da dama sun yi zanga zanga da sukai wa lakabi da “Tattakin Haraji” a birane fiye da Dari a fadin Amurka domin nuna rashin jin dadin su bisa kin bayyana takardun harajin da Shugaban yaki, Inda suke cewa sai dai in shugabn na boye wani abune da baya son a gani.
Trump yayi kwana daga katafaren Mar-a-Lago dake Forida da alamun bayasan haduwa da masu zanga zangar a West Palm Beach.
Biranen da Masu zanga zangar suka hadu sun hada da Washington, da Philadelphia da Chicago da kuma New York. An tsare mutane da yawa a Berkeley dake jihar California a yayin da masu zanga zanga biyu dake adawa da juna suka hadu suka fara jefa kwalabe da gami da naushin juna.
Yun da Trump ya shiga Office a watan Janairu, ya fadawa Yan jaridu cewa mutanen Amurka basu damu ba idan ya bayyana takardunsa na Haraji ba. Masu zanga zangar ta jiya Asbar ta nuna rashin yarda da maganar shugaban .
Facebook Forum