‘Yan kasar Turkiya na kada kuri’ar rabagardama domin maida Shugaban kasa mutum mai cikakken iko don fita daga tsarin zaben Firaminista na tsarin ‘yan Majalisar Dokoki. An bayyana zaben dai a matsayin zaben da yafi kowane zabe muhimmanci cikin shekaru 84 na shekarun tarihin kasar.
Zaben raba gardamar dai yaraba kasar da magoya baya da kuma masu suka wadanda suke kallon kasar zata shiga cikin hadari anan gaba. A yankin Kadikoy dake Istanbul ana gudanar da zaben cikin sauri da kuma kazar kazar tun da aka bude runfunan kada kuri’ar.
Wani mutum ya bayyana cewar “Na zabi A’a” domin babu wani abu makamancin haka a tsarin mulki na duniya kamar wanda suka gabatar mana yanzu. Babu ma’ana ta tarayya a cikinsa, Ba Demokradiyya bane, Babu komai ciki, Ace an tattara karfin mulki akan mutum guda, Misali idan wannan shugaban kasar tamu mutumin kirkine, nag aba fa? Ya kara da cewa Kowa zai iya amfani da wannan damar ta mummunar hanya.”
Yankin Kodikoy dai a Al’adance yanki ne da masu adawa da Shugaban kasa Tayyip Erdogan, wanda yake kan gaba wajen Kamfe din samar da Chanjin. Wata mata da ta kada kuri’a tace “ Nakada kuri’a ne doming aba. Bana son mulki yazama a hannun mutum gida, koda kuwa yana aiki ko baya aiki sosai, domin duk da haka muna da Yan majalisu da Ma’aikatan Shari’a da masu Yanke hukuncin Mulki masu zaman kansu. Ina bukatar irin wannna mulkin ya cigaba.
A daya bangaren kuwa akwai masu son ganin an canza tsarin kundin mulkin . Wani mai zabe yace “Na zabi E” domin amfanin kasata.
Erdogan ya matsau a yi gyaran tsarin mulkin domin samun damar tafiyar da gwamnatin cikin tsrai wanda zai baiwa Turkiya damar fuskantar Matsalolin yaki da Yan ta’adda da kuma jan ragamar tattalin arziki.
Facebook Forum