Mai baida shawara kan harkokin tsaron kasa na Amurka H.R. McMaster ya isa Kabul a yau lahadi domin tattaunawa da Shuwagabanin Afghanistan akan harkokin tsaro da kuma duba yanayin Dakarun Amurka dake kasar.
Ziyarar Mc.Master ta biyo bayan kiran da Kwamandojin Sojin Amurka suka yin a Karin dubaunnan sojojin Amurka a kan Sojoji 8,400 dake Afghanistan a yanzu haka domin karya lagon hare haren ‘Yan kungiyar Taliban.
Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya tarbi McMaster a Kabul inda ya yi masa godiya bisa cigaban tallafin da Amurka ke baiwa Afghanistan.
A wani gajeren bayani da fadar gwamnatin kasar Afghanistan ta bayar a rubuce bayan tattaunawar tace “Ghani da McMaster sun tattauna akan dangantakar dake tsakanin Kasashen guda biyu da suka shafi harkokin Tsaro, Yaki da Ta’addanci, Farfadowa da kuma Gina kasa”.
Mataimakin shugaban Sojojin kasar Afghanistan, Janar Murad Ali Murad, ya tabbatarwa da manema labarai cewa McMaster ya hadu da takwaran aikinsa Hafneef Atmar bayan saukar sa a Kabul. Murad yace ziyarar babban jami’in na Amurka ta nuna irin karfin da dangantakar dake tsakanin Amurka da Afghanistan ta kawar da “Makiyansu” wato ‘Yan ta’adda.
Facebook Forum