Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunkurin Gwamnatin Najeriya Na Daukar Matasa Aiki Ya Samu Cikas


BORNO: Ziyarar kwamitin sa ido na Majalisar Dattawa akan harkokin IDPs
BORNO: Ziyarar kwamitin sa ido na Majalisar Dattawa akan harkokin IDPs

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara daukan matasa aiki kamar yadda ta yi alkawali, amma yunkurin ya samu cikas a jihohi da dama a shiyar Arewa mussamman a Jihar Neja da Borno da Adamawa da Katsina da Kano da Kebi da kuma jihar Zamfara.

A watan jiya ne gwamnatin tarayya ta fitar da jerin sunayen matasa dubu 200, wanda tace sun sami nasarar shiga kashin farko na shirin da gwamnati tayi don tallafawa matasa marasa aikin yi.

Sai dai shirin ya gamu da korafe korafe a yawancin jahohin Arewa musamman a jahar Borno inda da rikicin Boko Haram ya dai dai ta. Sanata Baba Kaka Bashir Garbai, mai wakiltar Borno ta tsakiya a Majalisar Dattawa, yace an kware su a jahar Borno domin ana amfani da yanar gizo ne wajen yin rijistar masu neman aikin. Sai dai jihar Borno na fama da matsalolin hanyoyin sadarwa da wutar lantarki.

A bangaren Majalisar wakilai Mohammed Tahir Mongono, daga jahar Borno yace mutum biyu kadai aka dauka daga karamar hukumar da yake wakilta, sai dai yace sun dauki mataki kasancewar sune wakilan mutane inda suka kai kuka ga hukumar dake kula da wannan shiri.

A cikin matasa dubu 200 an dauki dubu 150 a matsayin malaman makaranta, dubu 30 kuma zasu yi aiki a fannin Noma. Yayin da ragowar dubu 20 zasu yi aiki a fannin Kiwon lafiya.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG