Taron da aka sa masa lakabin "Ana bukatan karin mata a harkokin siyasar Afirka an rufeshi yau bayan mata daga kasashen Afirka goma sha biyar sun kwashe kwanaki uku suna tattaunawa akan yadda zasu kara samun mukaman siyasa a kasashensu.
Kasar Kamaru da ta zama mai masaukin baki tana da doka da ta tanada wa mata wasu mukaman siyasa. Cikin kundun tsarin mulkin kasar mata nada akalla kaso talatin cikin dari da duk mukaman siyasa da na gwamnati.
Wata da ta halarci taron daga kasar Ivory Coast tace a kasarsu ko kashi goma basu dashi a hukumance kamar Kamaru.Amma ta yi fatan kasarta zata yi koyi da sauran kasashe koda ma na majalisar dokokin kasar.
Daga kasar Togo wata ma tace su ma suna cikin gwagwarmaya da gwamnatin kasarsu domin samar wa mata kaso mai tsoka.
Wata ma daga kasar Faransa tace yakin da kasarta ta keyi ke nan domin baiwa mata hakokinsu ta yadda zasu yi aiki kafada da kafada da sauran takwarorinsu maza walau ta fanin siyasa ko aikin gwamnati.
Kasashen nahiyar Afirka kasashe ne da basa kula da hakokin mata. Matar da ta zo daga Faransa tace lokaci ya yi da Afirka zata tashi ta ba mata hakokinsu ta kuma kare muradunsu. Tace zasu tsaya tsayin daka su tabbatar mata suna samun hakokinsu a Afirka.
Ga karin bayani.