Jami'an sojojin kasar sun ce wasu maza biyu ne suka shiga kasuwar Meme yau Juama'a suka tarwatsa kansu.
Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin amma Hausawa sun ce biri ya yi kama da mutum saboda haka harin yana da kwatancin irin harin da kungiyar Boko Haram ta Najeriya ke kaiwa.
Hare haren da aka dorawa alhakinsa kan ita kungiyar Boko Haram kaiwa kasar Kamaru sun kashe fiye da mutane dubu a arewacin kasar tun shekarar 2013.
Kamaru tana cikin kawancen kasashen yankin da aka kafa domin yakar Boko Haram. Kasashen dake cikin kawancen sun hada da ita Kamaru da Najeriya da Chadi da Nijar sai kuma jamhuriyar Benin.
A farkon wannan makon Kamaru ta sanar cewa dakarunta sun kwato garin Goshi dake arewa maso gabashin Najeriya daga 'yan Boko Haram kuma sun kashe fiye da mayaka 160
Sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya tare da kungiyar Amnesty International suka fitar sun ce cikin shekaru shidan da kungiyar Boko Haram ta yi tana tada karin baya ta hallaka mutane fiye da 20,000 kana ta yi sanadiyar wasu mutane miliyan biyu da dubu dari biyar rasa muhallansu