A cikin wannan makon sau iyu ke nan 'yan Boko Haram suna kai hari a garuruwan jihar arewa mai nisa.
Bisa ga duka alama maharan kungiyar Boko Haram sun kara zafafa kai hare-hare a kasar Kamaru musamman a arewacin kasar.
Cikin duka kasashen dake yankin tafkin Chadi yanzu kasar Kamaru ce ta fi samun hare hare daga kungiyar Boko Haram, musamman harin kunar bakin wake.
Ma'ala Bukar dan asalin garin Kirawa yace ko sojoji na garin ba zasu iya yin komi ba saboda 'yan kunar bakin waken suna bar da kama ne yanzu yadda ba'a iya ganesu..
Baba Gana Shettima wani mamba n kungiyar kwato hakin dan Adam ne a yankin arewacin kasar ta Kamaru yace alamuran dake faruwa sun tsorata mutane. Babu kwanciyar hankalin gudanar da abubuwa domin babu wanda ya san wuri ko lokacin da bam zai tashi.
Kodayake jami'an tsaro na iyakacin nasu kokarin duk da haka suna bukatar taimako. Wani Ibrahim Jika tsohon jami'in tsaro ne yace idan Kamaru bata canza yanayin dakarun tsaronta ba wankin hula ka iya kaita dare.
Ga karin bayani.