Kasar Faransa ta ba wa kasar Kamaru taimakon kayan yaki da su ka hada da motoci 12 masu sulke da riguna suma masu sulke duk a matsayin gudunmowar yaki da Boko Haram.
Jakadiyar Faransa a Kamarun Christele Robinson da ke zaune a Younde ce ta mika gudunmowar a madadin kasar ta Faransa.
Da ya ke amsar kayan yakin a madadin gwamnatin Faransar, Ministan Tsaron Faransa Joseph Beti Assomo ya yaba ma kasar ta Faransa da wannan gudunmowar , ya ce wannan na nuni da irin yadda Faransa ke ba da himma a yaki da Boko Haram, 'yan ta'addan Najeriya mai makwabtaka da Kamaru, wadanda kan kai hare-hare a arewacin Najeriya da makwabtan kasashe.
Ga wakilinmu Garba Awwal da cikakken rahoton: