Wani matashi da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyanawa wakilinmu Muhamad Awal Garba cewa, abin ya faru ne a lokacin da ‘yan sanda suka aiwatar da kamen wani matsahi da sunan barawo ne shi har ma suka harbe shi a kafarsa.
Daga nan ne bayan kai matashin asibiti sai yace ga garinku na, ma’ana ya mutu. Wannan ne ya harzuka matasa har suka fito zanga-zanga, musamman da suka gane cewa wannan matashi da aka zarga da sata ba shine barawon ba.
Garin yin wannan zanga-zanga ne ‘yan sandan suka sami karon battar da matasan da suka botsare da cewa sai an yi adalci game da kashe natashin da suka yi sanadiyyar harbin bindiga. An kakkama mutane da yawa amma hakan bai hana ci gaban boren ba.
Wakilinmu ya ji ta bakin masu jama’ar da suke ganin ya kamata kasar ta Kamaru fa ta bi a hankali don gudun kar allura ta tono garma. Ga cikakken sautin rahoton a kasan wannan shafi.