Ministan kudin Kamaru Hananiah Usman shi ya gudanar da taro da kamfanonin gwamnati da 'yan kasuwa .
An gudanar da taron ne a babban zauren shawara na kasar dake Younde babban birnin jamhuriyar.
Jadawalin taron shi ne ganin yadda gwamnatin kasar zata habaka tattalin arzikinta musamman yanzu da farashin man fetur ya fadi. Kashi hamsin na arzikin kasar ya ta'allaka ne akan albarkatun man fetur.
Rigingimun da Boko Haram ke haddasawa cikin kasar ya sa tana kashe makudan kudi kan harkokin tsaro. Saboda haka ministan kudi ya gargadi kamfanoni su dinga biyan harajinsu ba tare da bata lokaci ba domin ta dogara a kai ne.
Gwamnatin kasar ba zata yi sakosako ba da harkokin tsaro. Mr Emmanuel wani wakilin cibiyar kasuwanci ya kira gwamnati ta sa idanu a harkokin tattalin arzikinta da yanzu suke tangan tangan.
Ga karin bayani.