Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayin 'Yan Takarar Kujerar Shugaban Jamus Ya Yi Hannun Riga Akan Trump


German Chancellor Olaf Scholz records his New Year's speech at the chancellery in Berlin
German Chancellor Olaf Scholz records his New Year's speech at the chancellery in Berlin

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya ce idan Amurka ta kuskura ta kakaba wa tarayyar Turai haraji, a shirye Turai take ita ma ta mai da martani “cikin sa’a daya,”

Olaf Scholz ya bayyana hakan ne a wurin wata mahawarar da ake yi gabanin zaben kasar da abokin karawar shi mai ra’ayin mazan jiya Freidich Merz.

A mahawarar farko da suka yi gabanin zaben da zai gudana a ranar 23 ga watan Fabrairu, Merz ya bayyana Scholz a matsayin wanda bashi da azama, wanda ya jefa Jamus cikin matsalar tattalin arziki, yayin da dan jam’iyyar Social Democrat din ya bayyana kanshi a matsayin shugaba wanda ya kware kuma mai azama.

Da aka mishi tambaya akan ko tarayyar Turai ta shirya martanin ta akan laftawa mata haraji da Amurka take barazanar yi, Scholz, wanda yake bayan Merx da kuri’u, ya ce, “kwarai, zamu iya mai da martani cikin sa’a daya.”

Shugaban Amurka Donald Trump, ya sha yin barazanar kakabawa abokiyar cinikayyar Amurka mafi girma, haraji tare da zargin ta da amfana da arzikin Amurka.

Alhakin kula da al’amuran dokokin kasuwanci mai la'akari da cancanta, alhakin Tarayyar Turai ne karkashin hukumar Turai a Brussels.

Trump da wanda ake ganin ya fi dacewa da zama takwaran shi a Jamus, duk sun samu goyon bayan aminin shi Elon Musk, wanda ya mamaye batun mahawarar.

Merz, wanda yake kan gaba a kuri’u sannan wanda hankali ya fi karkata akan ya zama shugaban Jamus na gaba, ya nuna halin ko in kula akan lafta haraji ko kuma yin rance don cike gibin kudaden da NATO take bukata ta kashe don cika alkawarin kawancen ta na tsaro da ya kai kaso 2% na yawan kudaden shigan da take samu, wanda ya gaza kaso 5% din da Trump yake neman su ba Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG