Yawan mutane farar hular dake rasa rayukkansu a rikicin birnin Falluja na kasar Iraq na karuwa sosai yayinda yakin kwato birnin wanda ke hannun ‘yan ISIS ke kara tsananta.
“Wani bala’i ne yake faruwa a birnin yanzu haka. Rikicin ya rutsa da iyalai masu yawa kuma babu mafita," a cewar Jan Egeland (YAAN AY-guh-lan) na hukumar kula da ‘yan gudun hijirar kasar Norway.
Dakarun Iraki sun kaddamar da wani farmaki da niyyar kwato garin ne.
Akalla akwai yara 20,000 da rikicin ya ruttsa da su a cikin birnin, a cewar wata sanarwa da hukumar tallafawa asusun yara na Majalisar dinkin duniya, da ake kira UNICEF ta fidda. Hukumar ta yi kira ga duk bangarorin da ke fafatawa da su tabbata sun kare rayukan yaran, wadanda ke cikin hadarin a iya maida su sojoji.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta ce ta sami rahotanin da suka nuna cewa ana kashe fararen hula a barin wuta ko kuma baruguzan gidaje su binne su.
Akwai kuma rahotannin da suka nuna cewa ‘yan ISIS na amfani da Daruruwan iyalai wajen yin garkuwa da su, a cewar mai magana da yawun hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijirar William Spindler.
Wasu iyalai su 625 sun sami sa'ar kubuta da ficewa daga wannan fadan cikin makon da ya gabata.