A wani kiyasi da hukumar lafiya ta duniya ta fitar ya nuna cewar kimanin mutane Miliyan Shida ne ke mutuwa a duk shekara, a dalilin kamuwa da cututtuka dake da nasaba da shan taba sigari.
Taken bukin na bama dai shine hana yiwa kwalayen sigari kwalliya domin rage sha’awarsu, abinda hukumar lafiya ta duniya tace zai taimaka wajen rage shan taba sigari a duniya.
Shugabar hukumar lafiya ta duniya Margaret Chan, tace fatan hukumar shine ganin cewa gwamnatoci daban daban na kasashen duniya sun sa ido kan kamfanonin taba sigari don ganin sun rage irin adon da sukeyi kan kwalayen sigari, ta yadda hakan zai rage daukar hankalin jama’a musamman ma matasa wajen zukar tabar sigari.
Kawo yanzu dai binciken Likitoci ya nuna cewa tabar sigari na kunshe da akalla sinadarai kimanin 600 wanda kuma idan aka kona zasu fitar da wasu sinadarai kimanin 7000 masu cutarwa ga bil Adama, wanda kuma akasarinsu ke haifar da cutar daji wato Cancer a turance.
Sai dai masu iya magana na cewa idan kunne yaji to jiki ya tsira.
Domin karin bayani.