Zanga-zangar ta cigaba a jihohin Anambra, Abia, Enugu da birnin Asaba a jihar Delta.
An samu arangama tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar Biafra da tayi sanadiyar rasa rayuka da jikata wasu.
Zanga-zangar dai, ta tunawa ce da ranakun yakin basasa inda 'yan Najeriya da dama suka kwanta dama musamman 'yan kabilar Igbo.
Zanga-zangar ta jiya ta haifar da damuwa ga al'ummomi daban daban da suka fito daga wasu wurare a Najeriya dake zaune a yankin sun shiga wani halin rudu domin suna zaman dar dar..
Wani da ya yi magana da Muryar Amurka yace 'yan Biafra ne suka fito suka tarwatsasu. Ko 'yansanda da suka yi yunkurin tarwatsa masu zana-zangar sai da suka fasa masu motarsu suka fatattakesu kana suka ji ma wasu mutane ciwo saboda 'yansandan dole suka gudu..
To saidai 'yan arewa dake bakin kasuwa sun taru sun kori masu zanga zangar yayinda suka yi yunkurin kai har kan kasuwarsu.Haka ma 'yansandan da suka kawo doki sun tarwatsasu.
An yi mummunan arangama tsakanin jami'an tsaro da 'yan rajin kafa kasar Biafra har ma an samu hasarar rayuka tare da jikata wasu.
Rundunar 'yansandan Niger Delta ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai da suka hada da jami'anta guda biyu. Su ma 'yan kungiyar Biafra sun yi hasarar mutane hudu.
Usman Baba Alkali kwamishanan 'yansandan jihar Delta yace da suka fito a Asaba sun yi kokarin ketare gada su shiga Onitsha sai 'yansanda suka datse gadar amma basu san 'yan Biafran sun fito da makamai ba. Nan ne rikici ya barke.
Ga karin bayani.