Yau ne ake sa ran ‘Yan kasar Holland suke jefa kuriaar amincewa ko kuma akasi na goyon bayan kungiyar tarayyar Turai akan samar da cinikayya da kasar Ukraine.
Wannan kuriar jin ra'ayin jamar ba wai ya zame tilas bane ayi aiki da ita, amma yana da muhimmamci domin gane irin goyon bayan da kungiyar take dashi, kuma sai gashi wannan yana zuwa watanni ukku da lokacin da kasar Birtaniya ta jefa kuria'ar amincewa na ko taci gaba da zama cikin kungiyar ta tarayyar turai ko kuma a’a.
Masu banbancin raayi da kasar ta Holland da kungiyar ta Tarayyar Turai sunce tana kokarin ganin ta kawo Ukraine, ne wacce ke kokarin ganin ta shawo kan cin hanci da rashawa da ya addabe ta da kuma matsalar ‘yan aware.
Masu goyon bayan ta suka ce wannan zai iya taimakawa kasr ta fannin tattalin arzikin ta kana ya kara inganta ‘yancin dana dam a kasar.
Yanzu haka dai shugaban kasar na Ukraine Petro Poronshenko ya bukaci yan kasar ta Holland dasu jefa kuriar cewa sun amince da wannan yarjejeniyar.