Bincike da muryar Amurka ta gudanar ya nuna takaddamar ta samo asali ne daga karar da aka kai caji ofis na batar wayar salula, dalilin da ya yi sanadin tsare ‘yan garuwan goma sha takwas na tsawon yini guda.
Abin da ya fusata ‘yan Garuwan inji Mallam Adamu Ibrahim, wani daga cikin ‘yan Garuwan shine kudin beli na naira dubu uku-uku da jami’an ‘yan sanda na ofishin DPO na Yolde Pate, suka karba daga kowannen su, kafin su sakesu bayan ba a sami ko da dayansu da aikata laifi ba.
Ko da wakilinmu Sanusi Adamu ya nemi ya jita bakin mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa Alhaji Modu, kan wannan batun wanda ya ce bashi da wata masaniya, amma zai bincika ya kuma kira shi. Daga bisani dai bai kira shi ba, kuma ya ki daukar wayarsa lokaci da ya kira shi.
Wani mazaunin anguwar mararrabar Yolde Pate Malllam Abubakar Ahmed, ya nuna takaicinsa da yadda ‘yan sanda suke amsar kudin beli duk da cewar magabatansu suna nanata ba a biya kudin belin, lamari ya ce ya jefa dubban mazauna anguwar cikin mawuyacin hali game da barazanar kaura daga anguwar da ‘ya garuwan ke masu.
Domin karin bayani.