Emma Gwadal ya shaidawa 'yansanda cewa wani Dembo Akpa ne daga jihar Filato ke kera musu bindigogin.
DSP Abu Jinjiri kakakin 'yansandan jihar Jigawa yace sun kama shi Sylvesta din wanda ya yadda shi ne za'a kaiwa bindigogin amma basu samu nasarar kama mai kerawa ba.
Bayan sun kammala bincike sun gurfanar da mutanen biyu gaban kotu. Yanzu suna fuskantar shari'a.
Sakamakon binciken da 'yansanda suka yi bai nuna mutanen nada alaka da 'yan Boko Haram ba ko kuma wata kungiya ta 'yan fashi da makami.
'Yansanda na tuhumar mutanen biyu da laifin mallakar makamai ba kan ka'ida ba. Mallakar irin wadannan makaman ba tare da lasisi ba laifi ne.
To cajin da ake yiwa mutanen biyu ka iya canzawa saboda har yanzu basu cafke mai kera makaman ba. Tana yiwuwa idan an kamashi wasu bayanai su canza da ka iya kaiga canza cajin da ake yi masu yanzu.
Tun farko babban sifeton 'yansanda Najeriya Solomon Aease ya bada umurnin kara wa'adin sabunta lasisin mallakar bindigogi zuwa watan gobe.Bayan wa'adin duk wanda bai sabunta nashi ba 'yansanda zasu soma kamasu
Ga karin bayani.