Duk da hasashen yiwuwar rikici, jigilar bakin a jiya ta yiwu lami-lafiya a Lesbos din, in ka dauke wasu tsirarun masu zanga-zangar nuna adawa da yarjejeniyar da suka taru a gabar tekun. An dai fara dibar bakin ne a cikin motar safa a yammacin shekaran jiya daga sansanin dake Moria, zuwa gabar tekun Mytlini inda jiragen ke jiransu.
Wani jami’in Girka ya fadawa Muryar Amurka cewa, mutane 202 ne suka fara yin gaba a cikin jiragen ruwa guda 3. Sai kuma wasu jirage biyu dauke da mutane 136 suka bi bayansu. Jirgi daya kuma mai dauke da mutane 66 ya tashi ne daga tekun Chios a jiya Litinin.
Jami’in ya bayyana cewa, wadanda aka fara yin gaba da su din sun shigar da koken neman mafaka ne, sannan kusan gaba dayansu ‘yan asalin kasar Pakistan ne, in ka dauke wasu ‘yan Syria guda 2 da suka zabi Turkiyya bisa dalilan da su ke da nasaba iyalansu.