An ba Agusta Uwanmanzu-Nna, wadda ‘iyayenta suka kaura zuwa Amurka daga Najeriya, daga nan zuwa daya ga watan Mayu ta zabi makarantar da take so ta tafi daga cikin fitattun jami’oin Amurkan.
Bara wani dalibi haifaffen Najeriya Harold Ekeh ya zabi zuwa jami’ar Yale bayanda aka dauke shi a duka fitattun jami’oin takwas.
Duka dabilban biyu sun yi karatu ne a makarantar sakandare ta Elmon Memorial dake New York.
An kuma dauki Uwamanzu-Nna a wadansu karin jami’oi hudu da ta nemi shiga da suka hada da Jami’ar John Hopkins, Jami’ar fasaha ta Massachusetts, jami’ar New York ko NYU da kuma makarantar fasaha ta Resselaer.
Uwamanzu-Nna ta shaidawa wata tashar talabijin cewa, “ko da yake an haifeni a nan Amurka, na ziyarci Najeriya a lokuta da dama. Na kuma ga ‘yan’uwana da basu da irin wannan damar da na samu. Saboda haka, dukan abinda nayi, zan tabbata ya daga mutumcin Najeriya.”