Duk da cewa da alamu guguwar zaben fidda gwani tsakanin masu neman takarar shugabancin Amurka ta lafa, yunkurin da dukkanin ‘yan takara a tsakanin jam’iyyar Republican da Democrat ke yin a ganin sun samu nasara, na ci gaba da zafafa.
‘Yar takara a karkashin jam’iyar Democrat wacce kuma ita ke kan gaba, Hillary Clinton, ta sha kayi a hanun Bernie Sanders a zabukan da aka yi ranar Asabar a Jihar Washington da Hawaii da kuma Alaska.
Sai dai duk da wadannan nasarori na Sanders, har yanzu akwai babbar tazara tsakaninsa da Clinton da kusan wakilai 300.
Amma kuma a daya bangaren nasarorin, kwarin gwiwa ne ga yakin neman zaben Sanders, wadanda ka iya zama sharar fage ga yunkurinsa na samun nasara a nan gaba.
A ranar biyar ga watan Aprilu mai kamawa, ‘yan Democrat za su sake wani zaben a Winsconsin sannan sai kuma ranar 9 ga watan na Aprilu su sake fafatawa a jihar Wyoming da ba ta da yawan jama’a.