‘’Kusan karfe ukku saura na samu labarin nan, ance mun ma wajen karfe goma sha biyu ta tashi, ina jin labari ban zame ko in aba sai gareji nan a bude cikin daren nan haka na fito,situttuka na guda biyu a saman nan suna cike da kaya dake sama nayi kokarin fasa wurin ni da wani makwabci na amma abin ya gagara tun cikin daren, ana cikin haka ne sai jamaa suka ankarar dani wuta ta mamaye kasar benen nan baki daya, lokacin da nazo da akwai ruwa a kusa da nace hasarar komi ba zanyi ba’’
‘’Mu munzo ba abinda muka dauka a kayan mu ina da shago guda daya.’’
‘’Ni fata ta ALLAH Ubangiji ya mayar muna da abinda ya faru domin ba abinda zamu ce da Ubangiji sai godiya tunda shi yaso mu da haka ba abinda na fitar dashi.’’
‘’Ko tasi ban dauka ba ba abinda na dauka.’’
‘’Runfuna fiye da dubu sun riga sun kone, kuma wutar sai gaba take ci kuma ba abinda aka tsira dashi duk wanda yake nan yankin ba wanda ya tsira da wani abu.’’
‘’Ni dai ban samu sakamakon samun labari ba sai wayewar gari da safe, kuma nazo na taras da runfata ta kone gaba daya.’’
Wasu daga cikin ‘yan kasuwan da wannan balain ya rutsa dasu Kenan.
Babban kalubalen da aka fuskanta shine na rashin jamian kwana-kwana da masu bada agajin gaggawa.
Rashin kayayyakin aiki ya taimaka wajen bazuwar gobarar zuwa wasu sassan kasuwar
Ga Mahmu Ibrahim Kwari da Karin bayani