A Iraqi dakarun kasar sun fuskanci turjiya mai tsanani, a matakin farko da suka dauka na kai farmakin kwato birnin Mosul dake zaman tungar 'yan kungiyar ISIS.
Da misalin karfe 6 na safiyar jiya alhamis ne sojojin Iraqi su kimanin dubu hudu suka fara dumfarar wasu kauyuka masu tazarar kilomita 75 a kudu maso gabas da birnin Mosul. Dakarun Kurdawa da ake kira Pershmerga sun ce mazauna wasu kauyukan sun fice.
Wani wakilin MA dake fagen daga, ya lura cewa sojojin sun tinkari kauyukan daga kusurwoyi biyu. Zuwa tsakar ranar jiya, sojojin sun kwato kauyuka hudu, amma har yanzu ba zasu iya yin ikirarin iko akan su ba. Kamar yadda Janar Najat Ali na mayakan sakan kurdawa ya gayawa MA,
"Sojojin na Iraqi sun kaddamar da farmaki, amma da suka kai ga wadannan kauyuka, sai mayakan ISIS suka kai musu hare-hare na 'yan kunar bakin wake, da bindigogin igwa,da ire iren wadannan makamai. Saboda haka wannan ya sa sojojin na Iraqi sun tsaya."
Wadannan sojoji na Iraqi sun fito ne daga wasu birged guda biyu dake karkashin runduna ta 15 ta Iraqi wadda Amurka ta horas. Haka kuma a cikin wannan farmaki, akwai mayaka daga kabilu 'yan mazhabar sunni. Wadanda dakarun na Peshmerga suka ce yana da muhimmanci su kasance cikinsu domin samun nasarar rike yankunan da za a iya kwatowa wadanda duk na 'yan Sunni ne.
Wadannan sojoji na Iraqi sun fito ne daga wasu birged guda biyu dake karkashin runduna ta 15 ta Iraqi
WASHINGTON, DC —
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024