Yawaitan hadduran akan titunan Najeriya, na jawo damuwa a zukatar al’uma dake zirga zirgakan tituna inda zuciyarsu kanyi dar dar masamman ma a yankunan da suka yi kaurin suna wajen samun hadari.
Kama daga kwanar Langa Langa, a jihar Nasarawa, hawan Kibo kan hanyar Jos, kwanar Mai Saje kan hanyar Adamawa, da wasu ramuka kan babbar hanyar Abuja, Kaduna zuwa Kano.
Harma da wata hanyar da ta zama ramuka daga Minna zuwa Kontagora, a jihar Neja, shin a iya gwada yawan rasa rayuka a sakamakon hadura da yawan wadanda ‘yan ta’adda kan kashe.
Abinda ya zama zahiri shine zai yi wuya kayi tafiyar kilomita goma baka ga wata mota a yashe a gefen titi da tayi hadari ba.
Mutuwar karamin Minista James Ocholi, kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, ta tado maganar rashin sahihancin lasisin tuki ga wasu direbobin, da dan majalisa Gudaji Kazaure, yake gani ya dace a samu doka mai inganci.