Faduwar farashin albarkatun Mai a kasuwar duniya shine ya tilassawa hukumomin Najeriya,inganta sauran fannonin tattalin arzikin kasar masamman ma sashen noma da nufin cike gibin da aka samu a bangaren kudaden shiga na Man fetur.
Dr. Shehu Ahmed, babban sakatare a ma’aikatar aiyukan noma ta tarayya yace yanzu Najeriya, ana so a koma noma kamar da bawai a lokacin damuna ba kadai za’a yi noma ba.
Yana mai cewa ana son noma ya kasance abin yin rani da damuna.
Dangane da haka ne Gwamnatin jihar Jigawa ta kebewa fanin noma kaso mai tsoka daga cikin kasafinta na bana na fiye da Naira biliyan dari da talatin, in ji Gwamna Badaru Abubakar.
A jihar Kaduna kuwa Gwamnati ce ta sauya tsarin bada taki ga manoman jihar inda tace maimakon damka takin a hannun sarakunar gargajiya da shuwagabaini siyasa a matakai daban daban.
A yanzu Gwamna el-Rufai, yace salon bada takin na kai tsaye ne daga Gwamnati zuwa manomin dake karkara.
Sai dai har yanzu manoman jihar ta Kaduna na kokawa kan rashin aiwatar da shirin bada rance na Naira biliyan daya da Gwamnatin Ramalan Yero, ta tsara gabanin mkarewar wa’adinta kuma Gwamna el-Rufai, yace za’a aiwatar dashi kamar yadda aka tsara shi a baya.
Ita kuwa Gwamnatin jihar Nijar ta fara gayyato kamfanoni ne daga waje domin su saka jari a bangaren noma na jihar in ji sakataren Labarai na Gwamna Jibrin Baba Ndace.
A jihar Kano kuwa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje cewa yayi za’a dauki noma tafkar sana’a ta kasuwanci ta yadda za’a dunga fitar da abincin zuwa kasashen waje.