A Ivory Coast, yanzu sojoji ne suke sintiri kan titunan birnin nan na 'yan yawon bude ido dake kan gabar teku da ake kira Grand Bassam Resort, kuma titunan suna nan wayam, kwana daya bayan da 'yan ta'adda suka kai hari a garin.
Ministan harkokin cikin gida Hameed Bakayoko, yace cikin wadanda suka halaka sun hada harda fararen hula 15, da sojoji 3. Haka nan yace duka maharan uku suma sun mutu. Amma rahotannin da aka samu tunda farko sun ce mahara shida ne suka farwa wurin yawon shakatawan.
Shugaban kasar Alassane Ouattara, a jawabin da ya yiwa al'umar kasar ta talabijin a daren jiya Litinin, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku
Shugaba Ouattara yace "gaskiya ne Ivory Coast tana tsaye daram. Tana tsaye domin yaki da ragaye da zummar kare jama'arta.