Ministan harkokin cikin gida Hamed Bakayoko yace wadanda suka mutu sun hada da farin kaya 15 da kuma sojoji uku. Ya kuma ce an kashe dukan ‘yan bindigan uku. Rahotannin farko sun ce ‘yan bindigan su shida ne.
Bakayoko ya yabawa jami’an tsaro domin daukan matakin gaggawa na kawo karshen harin, ya kuma ce, har yanzu suna kan bincike domin gano ko akwai wadansu ‘yan ta’addan da suka arce.
Kungiyar mayakan al-qaida a Maghreb dake da alaka da kungiyar Al-qaida ta arewacin Afrika ta dauki alhakin harin, da aka kai a wani otel dake birnin Grand-Bassam. Wannan ne karo na uku cikin watanni hudu da mayakan suka kai hare hare a otel-otel dake kasashen yammacin Afrika, bayan kazaman hare haren da suka kai a Burkina Faso babban birnin kasar Mali.
Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara ya ayyana makoki na kwana uku a wani jawabi mai sosa rai da ya gabatar ga kasa jiya Litinin da yamma.