Jiya da yamma a birnin Malabo fadar gwamnatin Equatorial Guinea gwamnatin kasar ta karrama Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da lambar yabo da tafi daraja mai suna Grand Collar of the Order of the Independence.
Bayan an bashi lambar Shugaba Buhari ya sadaukar da lambar wa kasarsa Najeriya da al'ummarta wadanda yace sun yi aiki tukuru babu kama hannun yaro \domin tabbatar da zaman lafiya a kasar ta Equatorial Guinea da ma Afirka gaba daya
Shugaba Buhari yace "ina son na mika matukar godiyata da ta mutanena da lambar yabon da aka bani"
Yayinda ake karramashi Shugaba Buhari ya ciga da cewa "Babu wani zarafi da yafi wanda muke dashi yanzu wajen karfafa dankon zumuncin makwaftaka a nahiyarmu ta Afirka domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro da tattalin arziki mai dorewa"
Shugaban yace yayinda kasashen Afirka ke fuskantar kalubale kusan iri daya kamata yayi su yi kokari su hada karfi da karfe su lalubo hanyoyin fita da zasu taimaka su hanzarta ci gaban tattalin arziki da na alummomin nahiyar.
Shugaba Buhari ya yi alkawari cewa a karkashin shugabancinsa, Najeriya zata cigaba da bada gudummawa wurin tabbatar da zaman lafiya da harkokin siyasa masu dorewa da cigaban Afirka.
Mai masaukinsa Shugaba Obiang Nguema Mbasogo na Equatorial Guinea da yake mayar da martani yace kasar ta karrama Shugaba Buhari saboda mutuncinsa da shugabanci nagari da hazaka da jaruntaka wurin yaki da cin hanci da rashawa da ta'addanci da nufin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka.
Saboda haka muka ga yakamata kuma abun yi ne mu karrama wannan babban dan Afirka domin manyan ayyukan da yake yi da suka hada da yaki da Boko Haram kungiyar da ta zamo kaya a makogwaron Afirka, inji Shugaba Mbasogo