A Rasha ma'aikatar tsaron kasar ta fada yau Talata cewa, tawagar farko ta jiragen yakin kasar sun bar Syria, bayan sanarwar d a shugaban kasar Vladimir Putin ya yayi na janye dakarunsa daga kasar bayan watanni biyar da rabi da suka yi a kasar Sham ko Syria.
Jirgin ya tashi daga sansanin mayakan sama dake lardin Latakia dake yammacin kasar kan hanyarsa zuwa Rasha.
Jiya Litinin shugaba Putin yace, "galibin" mayakan Rasha dake sham zasu bar kasar ganin yanzu an cimma burin abunda ya kai su.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya ko MDD na musamman kan rikicin na Syria Staffan de Mistura, yau Talata ya yabawa matakin da shugaba Putin ya dauka yana cewa "wannan muhimmin ci gaba ne," ya bayyana fatar hakan zai taimaka gaya wajen shawarwarin sulhu da yake shiga tsakani a Geneva.
Jakadan Angola a Majalisar Dinkin Duniya Ismael Gasper Martins,wanda shine yake rike da kujerar shugabancin kwamitin sulhu na karba karba, yace wannan mataki da Rasha ta dauka, da kuma komawa kan teburin shawarwari dangane da rikciin na Syria, ya nuna cewa "akwai canjin yanayi da kwamitin sulhu, na fatar ganin an sami "sakamako mai kayu."