Shugaba Buhari yace alkalai su ne suka zama masa kashin kifi a makogwaro wajen yaki da almundahana da cin hanci da rashawa da suka yiwa kasar katutu da hakan ka iya hanashi cimma nasara.
Babu mamaki yadda jam'iyyar PDP mai adawa ta kushewa matsayin shugaba Buhari tana zargin yana son ya yi anfani da yaki da cin hanci da rasgawa wajen murkushe 'yan adawa.
Kakakin PDP Oliseh Metuh dake zaman beli a halin yanzu ya nuna damuwa cewa jam'iyyarsu na fargaban gwamnatin yanzu zata yi rashin adalci a yaki da almundahana wanda yanzu yana gaf da tunkarar ofishin tsohoin shugaba Jonathan bayan samame bincike da hukumar EFCC ta kai ofishin tsohon mataimakinsa Namadi Sambo a Abuja.
To saidai tsoffin 'yan PDP da suka ce sun kashewa jam'iyyar kudi irinsu Alhaji Yahaya Bappa daga Borno na na'am da binciken jami'an tsohuwar gwamnatin. Ya yabawa EFCC amma yace suna wani kuskure. Wannan kuwa shi ne beli da ake ba wadanda aka kama da zargin sun yi almmundahana. Yace da zara an basu beli bayan shekara daya ko biyu sai maganar ta mutu.Yace kamata yayi a kamasu akan 'yan ta'ada.
A cewar wani shahararren mai sauraron Muryar Amurka Sale Bakaro Damaturu yakin yana da fa'ida amma ya jawo hankalin shugaban kasa da halin kunci da yace talakawa na fama dashi. Babu kudi a hannun jama'a sakamakon cewa kudi baya yawo. Kudin da ake kwatowa daga hannun barayi a yi anfani dasu a gyara kasar domin a samu saukin rayuwa.
Jigon APC Inuwa Yahaya ya bada amsa ga yanayin da ake ciki yanzu. Yace yana fatan 'yan Najeriya zasu ba gwamnoni hadin kai musamman akan tsarin da zai sa 'yan kasa su samu dogaro da kansu.
Tabbas yaki da cin hanci da rashawa da almundahana zai ratsa kusan duk sassan gwamnati saboda sunayen mutane da dama da ake zargin sun wawure dukiyar Najeriya.
Ga karin bayani.