A wani taron manema labarai da yayi a Minna jihar Neja shugaban kungiyar na kasa Ardon Zuru Alhaji Muhammad Kirwa yace suna bin hanyoyin ganawa da bata garin dake cikinsu.
Yace sun yiwa matasan tayin ahuwa kamar yadda ya faru a Kano cikin 'yankwanakin da suka gabata.Alhaji Kirwa yace babu wata kabila da bata da bata gari. Su ne suka fito suka amince akwai bata gari cikin matasansu.
A Kano sun bi irin wannan shirin na yiwa matasan ahuwa kuma an samu nasara. Daukan matakin yin ahuwa ga wadanda suka amsa laifukansu da ahuwar da suka samu da yadda zaman lafiya da tsaro suka dawo Kano ya sa wasu gwamnonnarewa suka kuduri yafewa matasa.
Kungiyar Miyetti Allah ta soma kidigdigan hasarar da tayi sanadiyar rikicin Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Yace kungiyar Alayat da ta Fulani suka yi taro a Maiduguri na adadin abun da suka rasa. Yace ya tabbata nasu ya fi nasu saboda haka zasu hada alkalumma su mikawa kwamitin da gwamnati ta kafa a duba a ga wane irin gudummawa za'a yi masu.
Kungiyar ta soma wani sabon shiri na fadakar da makiyaya akan mahimmancin neman ilimin zamani.
Ga karin bayani.