Dakarun Kamaru sun samu kashe maharan Boko Haram sun goma sha biyar tare da cafke wasu guda biyu.
Wani dan garin Ashigashiya yayi tsokaci akan lamarin. Yace 'yan Boko Haram sun farmasu amma da taimakon Allah dakarun Kamaru sun fafata dasu, sun kashe wasu, sauran kuma sun arce. Yace an yi kashe-kashe da yawa ta bangaren Boko Haram.
Shi ma wani jami'in tsaro ya yi karin bayani.Yace yanzu sun sa kafar wando daya dasu, wato su 'yan Boko Haram. Sai sun ga bayan 'yan ta'adan.
Riwanu Sharubutu wani dan siyasa kuma mai bada shawara wa hukumar tsaron kasa yace sun canza salo domin yaki da wanda baka ganinshi da wuya. Yanzu da yake suna turo yara ne da bamabamai sun dauki wani mataki daban. Kasar na shirin daukan sabbin sojoji yara masu karfi.
Ahalin yanzu dai kasar tana kara matakan tsaro a duk fadin kasar har ma ta dauki karin soja wajen dubu biyar.
Ga karin bayani.