Ranar Talata 27 ga watan Agusta na shekarar 1991 gwamnatin mulkin soji a Najeriya ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta sanar da kirkiro karin jihohi 9 a kasar, kuma jihar Jigawa na daga cikinsu.
A ranar Juma’a majalisar ta yi wani taron gaggawa don tattauna halin da kasa ke ciki a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyar ta PDP a Kano a baya-bayan nan, lamarin da ya sa ta rabu gida biyu tsakanin Wali da Abacha.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, wanda shi zai jagoranci kwamitin ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja.
Hukumar NUC da ke kula da jami’o’in Najeriya ta ba shugabannin jami’o’in kasar umurnin su rufe sai bayan zabe.
Magoya bayan jam'iyun siyasa da za su fafata a zaben da za a gudanar wannan watan sun bayyana dalilansu na marawa jam'iyun baya da kuma dawowa daga rakiyar wadansu.
Tsohuwar jihar Arewa a karkashin Lord Frederick Lugard, ita ce ta koma jihar Arewa ta tsakiya a alif 1967 kafin daga bisani ta zama jihar Kaduna a 1975. A alif 1987 ne kuma aka cire jihar Katsina daga tsohuwar jihar ta Kaduna, wadda a yanzu ke da kananan hukumomi 23.
Hukumomin tsaro a Najeriya, sun ba da tabbacin cewa za a gudanar da zaben 2023 lami lafiya suna masu kore duk wani yunkuri da wasu ke yi musamman a kafafen sada zumunta wajen yada kare-rayi don ganin sun haifar da fargaba a zukatan mutane.
Duk da karin wa’adin da babban bankin Najeriya na CBN ya yi na kawo karshen amfani da tsoffin takardun naira, har yanzu jama’a a kasar na ci gaba da fuskantar matsalar karancin sabbin kudaden.
A yayin da ake daf da gudanar da manyan zabuka na shugaban kasa, ‘yan majalisun tarayya, gwamnoni, da na ‘yan majalisun dokokin jihohin kasar 36, akwai muhimman bayanai dabam-daban a kan jihohin Najeriya da irin abubuwan da suka bambanta su da juna.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta maida martani kan zargin da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufa'i ya yi na cewa wadansu hadiman gwamnati a fadar shugaban kasa suna yi wa jam'iyyar zagon kasa don hana ta samun nasara a zaben da ke tafe.
Domin Kari