A wata hira da manema labarai a Fadar Shugaban kasa, Ministan yada labarai Lai Mohammed, ya nanata matsayin shugaban kasa na cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali ne kawai wajen tabbatar da an yi sahihin zabe ba tare da nuna goyon baya ko tauye wani ba.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewa wasu a fadar shugaban Najeriya na kokarin hana jam’iyyar APC da dan takararta na shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, samun nasara a zaben shugaban kasa da za a yi a wannan watan.
El-Rufai ya bayyana hakan ne ranar Laraba a lokacin wata hira da gidan Talabijin na Channels.
Gwamnan ya jaddada cewa, wadannan mutanen suna so dan takararsu ya yi nasara a zaben fidda gwani na shugaban kasa, amma bai ci zaben ba.
Ya kara da cewa mutanen na kokarin ganin jam’iyya mai mulki da Tinubu sun fadi zabe.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, wasu a fadar shugaban na kokarin fakewa da burin shugaba Buhari na yin abin da ya ke ganin ya dace don su dakile damar jam’iyyar.
Game da batun canza fasalin kudin Najeriya, El-Rufai ya fadi cewa bai kamata sauran jama’a su wahala ba saboda matakin, ko tsarin ya sa jama’a su ji haushin jam’iyyar APC tunda ba ra’ayin jam’iyyar ko na dan takararta ba ne, ra’ayi ne na wasu a fadar shugaban kasa, a cewarsa.
Ya kuma ce ya kamata jama’a su sani tsarin sauya fasalin kudi ba na gwamnan babban bankin Najeriya ba ne, don ko a lokacin mulkin soja shugaba Buhari ya dauki matakin a asirce da nufin kama masu sama da fadi da dukiyar al’uma.
Gwamnan ya ce ko da yake shugaban na da ikon sake fasalin kudi, yin hakan a daidai wannan lokaci ba shi da fa’ida ta bangaren siyasa ko tattalin arziki.
Kalaman na El-Rufai dai na zuwa ne mako guda bayan da dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki ya ce akwai wani shiryayyen kulli na hana shi cin zabe.
Sai dai gwamnatin tarayya ta maida martani ne kan zargin da gwamna Nasir El-Rufai ya yi, ba abin da dan takarar jam'iyyar ya fada a wajen yakin neman zabe ba.
A lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar gwamnati a yayin wani taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Laraba, Ministan yada labarai Lai Mohammed ya kuma ce idan har akwai wanda ke neman dakile wani dan takara, to a hukumance gwamnati bata san da shi ba.
Saurari Rahoton Babangida Jibrin: