Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta gargadi ‘yan siyasa da su kauce wa yin kalamai marasa tushe yayin da ake kusantar zaben shugaban kasa, wannan na zuwa ne bayan da daraktan yakin neman zaben jam'iyyar APC ya zargi sojoji da dan takarar shugaban kasa na PDP da yunkurin yin juyin mulki.
A Najeriya wasu masu jefa kuri'a sun nuna gamsuwa da tsarin muhawara tsakanin ‘yan takarar mukaman siyasa, domin a cewarsu hakan zai ba su damar tantance wadanda ke da kudurin yi wa jama'a aiki idan aka zabe su.
Ranar Talata 27 ga watan Agusta na shekarar 1991 gwamnatin mulkin soji a Najeriya ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta sanar da kirkiro karin jihohi 9 a kasar, kuma jihar Jigawa na daga cikinsu.
A ranar Juma’a majalisar ta yi wani taron gaggawa don tattauna halin da kasa ke ciki a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyar ta PDP a Kano a baya-bayan nan, lamarin da ya sa ta rabu gida biyu tsakanin Wali da Abacha.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, wanda shi zai jagoranci kwamitin ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja.
Hukumar NUC da ke kula da jami’o’in Najeriya ta ba shugabannin jami’o’in kasar umurnin su rufe sai bayan zabe.
Magoya bayan jam'iyun siyasa da za su fafata a zaben da za a gudanar wannan watan sun bayyana dalilansu na marawa jam'iyun baya da kuma dawowa daga rakiyar wadansu.
Tsohuwar jihar Arewa a karkashin Lord Frederick Lugard, ita ce ta koma jihar Arewa ta tsakiya a alif 1967 kafin daga bisani ta zama jihar Kaduna a 1975. A alif 1987 ne kuma aka cire jihar Katsina daga tsohuwar jihar ta Kaduna, wadda a yanzu ke da kananan hukumomi 23.
Hukumomin tsaro a Najeriya, sun ba da tabbacin cewa za a gudanar da zaben 2023 lami lafiya suna masu kore duk wani yunkuri da wasu ke yi musamman a kafafen sada zumunta wajen yada kare-rayi don ganin sun haifar da fargaba a zukatan mutane.
Duk da karin wa’adin da babban bankin Najeriya na CBN ya yi na kawo karshen amfani da tsoffin takardun naira, har yanzu jama’a a kasar na ci gaba da fuskantar matsalar karancin sabbin kudaden.
Domin Kari