Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta sami nasarar cafke kwamishinan hukumar zaben ta kasa INEC na Jihar Adamawa, Hudu Ari, wanda ya yi riga-malam masallaci wajen ayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa tun ba'a kammala tattara sakamakon baki daya ba.
Sai dai gwamnan na Adamawa bai kama sunan wadanda yake ikirarin da su ya yi takarar ba.
Majalisar Darektocin Jam'iyar PDP sun ja hankalin Hukumar Zaben Najeriya ta kiyaye sauya sakamakon zaben jihar Adamawa bayan riga-mallam massalacin da wani jami'in Hukumar zabe ya yi
Jami’in tattara sakamakon zabe ya ayyana Idris a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kebbi ranar Lahadi 16 ga watan Afirilu.
An girke jami'an tsaro masu yawa yayin da jama’a suka nufi rumfunan zaɓe ranar Asabar don a kaɗa ƙuri'ar zaɓen gwamna a Yola babban birnin Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.
A farkon makon nan hukumar INEC ta ayyana dan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamna a jihar, wanda aka yi a ranar 18 ga watan Maris a Najeriya.
A ranar Talata ne jagororin manyan jami’iyyun adawa a Najeriya biyu suka shigar da kara a kan neman soke sakamakon zaben shugaban kasa na watan Fabrairu da suke kalubalanta, kamar yadda takardun kotu su ka nuna, domin fara wata shari’ar da ka iya daukar tsawon watanni.
A karar da ya shigar, Obi da jam’iyyarsa sun ce 'yan Najeriya ba Tinubu da Kashim Shettima suka zaba ba.
A Yayin Zabukan gwamnoni da ‘yan majalisun jiha a fadin Najeriya, wasu kungiyoyi sun bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori shugaban hukumar zaben Najeriya bisa zarginsa da bayyana sakamakon zaben shugaban kasa ba bisa ka’ida ba, ko kuma matasan kasar su shiga zanga-zanga.
An fara kirga kuri'a a wasu rumfunan zabe na kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna saboda yadda aka fara zaben gwamnoni da 'yan majalissa akan lokaci a mafi yawancin rumfunan zabe.
Masu kada kuri’a basu fita zabe yadda ya kamata ba a karamar hukumar Karu wadda ta fi yawan jama’a a jihar Nasarawa da ke makwabtaka da Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Siyasar ubangida, siyasar kudi da amfani da kayayyakin masarufi domin jan hankalin masu kada kuri’a na daga cikin manyan al’amura da manazarta kan harkokin siyasa ke cewa suna dakushe ci gaban dimokaradiyya a Afrika da sauran kasashe masu tasowa kamar Najeriya.
Domin Kari