Rashin fita zaben sosai bai rasa nasaba da yadda wasu masu zabe suka zauna a gida don juyayin sakamakon zaben shugaban kasa da dan takararsu bai samu nasara ba.
Margaret Emmanuel, da ke mazabar Masaka a karamar hukumar ta Karu ta yi korafin rashin samun ihsani duk da jurewa da ta yi wajen wakiltar daya daga cikin jam’iyyun da ke gwagwarmayar zama ko neman madafun ikon jihar.
Tun a shekarar 2011 babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta rasa gwamnatin jihar Nasarawa sanadiyyar faduwar marigayi Aliyu Akwe Doma, inda Tanko Almakura ya lashe zabe a karkashin jam'iyyar CPC, wadda ita ce jiha daya tak da CPC ta lashe kafin ta narke zuwa APC inda dan takarar gwamna mai ci A.A Sule ke neman tazarce, ita kuma PDP ta sake tsaida David Emmanuel Umbugadu.
Chief Aaron Dashe, mai anguwa ne na Rafin Kwara a Masaka, ya ce a jihar an samu sauyi saboda yadda jam'iyyar Labour ta yi tasiri a zaben shugaban kasa.
A Maraba bakin bankin Jaiz, a wata rumfa da ake sa ran sama da mutun 750 zasu kada kuri'a, kimanin mutun 100 ne suka fita zabe. Duk da haka wakilan manyan jam’iyyu sun nuna kwarin gwiwar samun nasara a karshen zaben.
A halin da ake ciki dai ‘yan Najeriya na kara fahimtar tasirin kuri’arsu, duk da cewa akwai dalilai da kan tura mutane su fito zabe ko su samu karayar gwiwa su zauna a gida.
Saurari rahoton Nasiru Adamu Elhikaya: