Jam'iyar APC mai mulki a Najeyatana ci gaba da fuskantar barazanar ficewar ‘ya'yanta zuwa wasu jam'iyu, daidai lokacin da jam'iyun ke faman samun jama'a don cin zabubukan shekara ta 2023.
Mataimakin dan takarar jam’iyyar APC na shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu wato Ibrahim Kabir Masari ya ce ko rana daya tak aka ba shi dama ya rike matsayin takarar ya gamsu.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce jam’iyyar su na maraba da wadanda za su so hada kai da su don babban zaben 2023
Ganin irin halin a ke fama da shi na rashin tsaro a Najeriya, babban abin da ke zukatan maniyatan hajjin bana, shi ne addu'ar neman mafita da kuma samun shugabanni na gari a zaben 2023.
Yayin da shirye-shiryen babban zaben 2023 a Najeriya ke ci gaba da kankama, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben. Atiku Abubakar dai ya sha yunkurin zama shugaban Najeriya a baya, ba tare da nasara ba.
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, dake neman tikitin kujerar shugaban Najeriya a zaben shekarar 2023 karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki ya ce jiga-jigan jam’iyyarsa zasu duba inda ya dace a fito da dan takara don kada PDP a zabe mai zuwa.
Yayin da ake ci gaba da samun masu bayyana kudurinsu na neman shugabancin Najeriya a zaben 2023, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwa ya bayyana dalilan da ya ce suka sa ya fi sauran masu kudurin tsayawa takara a karkashin jam’iyyar PDP cancanta.