Ganin irin halin a ke fama da shi na rashin tsaro a Najeriya, babban abin da ke zukatan maniyatan hajjin bana, shi ne addu'ar neman mafita da kuma samun shugabanni na gari a zaben 2023.
Yayin da shirye-shiryen babban zaben 2023 a Najeriya ke ci gaba da kankama, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben. Atiku Abubakar dai ya sha yunkurin zama shugaban Najeriya a baya, ba tare da nasara ba.
Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, dake neman tikitin kujerar shugaban Najeriya a zaben shekarar 2023 karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki ya ce jiga-jigan jam’iyyarsa zasu duba inda ya dace a fito da dan takara don kada PDP a zabe mai zuwa.
Yayin da ake ci gaba da samun masu bayyana kudurinsu na neman shugabancin Najeriya a zaben 2023, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwa ya bayyana dalilan da ya ce suka sa ya fi sauran masu kudurin tsayawa takara a karkashin jam’iyyar PDP cancanta.