Kotun dai ta amince cewa Lawal, bai shiga takarar fidda gwani ba na jam’iyyar ta APC , wanda aka yi a ranar 28 ga watan Mayun 2022.
Yayin da jam’iyyun siyasa suka yi nisa da yakin neman zabe na babban zaben 2023 a Najeriya, mun duba manyan alkawura ko manufofin manyan jam’iyyun siyasa hudu a kasar.
Madugun kamfen din samun tikitin dan takarar APC Bola Tinubu, Babachir David Lawan ya fito karara ya ce bai ga yadda Tinubu zai lashe zaben 2023 ba tun da bai dauki kirista mataimaki ba.
‘Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam’iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu yayi alkawarin ci gaba da inganta harkokin noma da samarwa matasa ayyukan yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiwatar.
Kotun har ila yau ta ba da umarnin a gudanar da sabon zaben fitar da gwani a jam'iyyar ta APC a jihar Taraba don fitar da dan takarar mukamin gwamna.
Jam’iyyar Lebour ta sanar da rasuwar mataimakin shugaban Jam’iyyar na Arewa ta Tsakiya, Adi Shirsha .
Kungiyar Gwamnonin Jam’iyar PDP G-5 ta kai ziyara wa Gwamnan Jihar Bauchi, Senata Bala Abdulkadir Muhammed, a matakin nemo hanyar sulhunta rikicin dake neman kawo baraka a tsakanin gwamnonin da kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyar.
PDP ta ce mutum 70 aka ji wa rauni, lamarin da ya kai ga kwantar da wasu asibiti.
A yau Laraba ne mataimakin darekta mai kula da sha’anin kwamfuta a hukumar INEC, Lawrence Bayode ya bada wannan tabbacin a hirar da ya yi da shirin “Sunrise Daily” na talabijin din Channels.
Hukumar zaben wacce ta kammala zagaye na karshe na sabunta rejistar gabanin babban zaben 2023, ta baiyana filla-filla irin matakan da ta kan bi gabanin yin rejistar.
Domin Kari