Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Kotun Daukaka Kara Ta Jaddada Machina A Matsayin Dan Takarar APC Na Yobe Ta Arewa


Ahmed Lawal, hagu, Bashir Machina, dama
Ahmed Lawal, hagu, Bashir Machina, dama

Kotun dai ta amince cewa Lawal, bai shiga takarar fidda gwani ba na jam’iyyar ta APC , wanda aka yi a ranar 28 ga watan Mayun 2022.

Kotun daukaka kara a Abuja, babban birnin Najeriya, ta jaddada cewa Bashir Sheriff Machina shi ne dan takarar jam’iyyar APC a zaben sanata a Yobe ta Arewa.

Kotun dai ta gaskata hukuncin da wata babbar kotu ta yanke a Damaturu babban birnin Yobe, wacce ta yanke hukuncin cewa ba shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawal ba ne dan takarar APC a zaben da za a yi a badi na mazabar Yobe ta Arewa.

Kotun dai ta amince cewa Lawal, bai shiga takarar fidda gwani ba na jam’iyyar ta APC , wanda aka yi a ranar 28 ga watan Mayun 2022.

Yayin yanke hukuncin a Abuja, Mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ta kwatanta zaben fidda da gwani da aka yi a ranar 9 ga watan Juni a matsayin haramtacce, wanda keta doka kamar yadda Channels ya ruwaito.

An dai dade ana kai ruwa rana kan wannan takaddama, lamarin da ya kai ga a wani lokaci a baya, Sanata Lawal ya mika wuya a watan Satumba inda ya ce ya janye.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na twitter, Lawal ya ce bayan tattaunawa da ‘yan siyasa, abokan huldarsa da magoya bayansa, ya yanke shawarar ba zai daukaka kara ba, yana mai cewa, ya amince da hukuncin kotun.

Ko da yake, daga baya, jam’iyyar ta APC reshen jihar Yobe ta ce za ta daukaka kara.

XS
SM
MD
LG