Bayode ya tabbatar da cewa babu wanda zai iya yiwa na’urar BIVAS kutse a ranar zabe.
“Ina so in kara tabbatar da cewa mun yi duk abin da ya dace don ganin cewa babu abin da zai taba na’urorin BIVAS. Za a tsare bayanan da ke kan BIVAS,” a cewar Bayode.
Ya kara da cewa bayan zaben, idan aka tura bayanai a cikin babban rumbun bayanan hukumar INEC, za a kare su.
Bayode ya kuma ce, ko muna so ko ba mu so, mutane za su yi kokari sosai don yi wa wannan tsarin katsalandan. Amma yayin da suke kokari, zasu ci gaba da cin karo da garkuwa mai karfi.”
“Zan iya cewa, mun kula da duk wani kalubale da ka iya shafar wannan tsarin, kuma mun yi iya kokarinmu don ganin ba za a iya kutsawa cikinsa ba a ranar zabe kuma zan iya nanata cewa ba za a iya satar bayanan cikin BIVAS ba," in ji shi.