Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP G-5 Ta Kai Ziyarar Sulhu Wa Gwamnan Jihar Bauchi 


Gwamnan Bauchi Bala Mohammed (Kauran Bauchi).
Gwamnan Bauchi Bala Mohammed (Kauran Bauchi).

Kungiyar Gwamnonin Jam’iyar  PDP  G-5 ta kai ziyara wa Gwamnan Jihar Bauchi, Senata Bala Abdulkadir Muhammed,  a matakin nemo hanyar sulhunta rikicin dake neman kawo baraka a tsakanin gwamnonin da kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyar.

BAUCHI, NIGERIA - Makasudin ziyarar ta gwamnonin G-5 din shi ne neman samun damar dinke barakar da ta faru a tsakanin gwamnonin G-5 din da ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyar, Alhaji Atiku Abubakar, da kuma jaddada wa gwamna Bala Abdulkadir Muhammed, goyon bayansu a fafutukar da yake yi na dawowa mulki a karo na biyu.

Gwamna Nyesom Ezenwo Wike na jihar Ribasa.
Gwamna Nyesom Ezenwo Wike na jihar Ribasa.

Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya ce munzo ne don yin sulhu da kuma sasanta tsakaninmu,ba mu kulle kofar sulhu ba, kugiyar gwamnonin G-5 ita ce kashin bayan jam’iyyar, ba za mu rufe kofar yin sulhu ba, a shirye muke a kowani lokaci don yin sulhu.

A daya hannun, Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya yi amfani da wannan ziyarar don neman gafara daga jama’a da suka nuna bacin ransu da wasu kalamai da yayi akan Fulani.

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom

Gwamnan na Jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ce ina so na fada cewa ba abin da nake nufi ba kenan, alokacin da aka same ni na fadi hakan, ina bada hakuri ga wanda kalamai na ya bata musu rai.

Daga bisani gwamnan Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed, ya yi karin haske kan ziyarar da gwamnonin G-5 din suka kawo Bauchi. Sannan wani jigo a jam’iyyar ta PDP, a Jihar Bauchi, ya jinjina wa gwamnan Bauchi, a kokarinsa na kawo sulhu tsakanin gwamnonin G-5 din da kuma Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa.

Saurari cikakken rahoton daga Abdulwahab Muhammad:

Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP G-5 Ta Kai Ziyarar Sulhu Wa Gwamnan Jihar Bauchi .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

XS
SM
MD
LG