Ofishin jakadancin Saudiyya a Washington ya jima yana nuna goyon bayan a fitar da bayanan sirrin don a kawo karshen zargin da ake yi wa masarautar, wanda ya ce “ba su da tushe.”
Kusan mutum 3,000 ne suka mutu a ranar ciki har da ma’aikatan kashe gobara da ‘yan sanda da suka kai dauki.
Mun yi waiwaye kan yadda aka kai wadannan hare-hare da suka sa Amurka ta mamaye Iraqi da Afghanistan domin yakar ayyukan ta’addanci.
A daidai lokacin da aka cika shekara ashirin da kai harin 9/11, Amurka ta kawo karshen yakin da take yi da kungiyar Taliban a Afghanistan. Sojojin Amurkan da dama sun rasa rayukansu a yakin, ciki har da Christopher Horton. Matarsa, Jane Horton, mai ba da shawara ce ga iyalan sojojin da suka mutu.
Shekaru ashirin kenan da kungiyar Al-Qaeda ta kaddamar da munanan hare-haren ta’addanci da jiragen sama a Amurka wanda aka fi sani da September 11. Birnin New York, yana daya daga cikin wuraren da harin ya fi muni, yayin da maharan suka dannan cikin cibiyar hada-hadar kasuwanci ta duniya...