Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Kun San Yadda Aka Kai Harin 11 Ga Watan Satumba A Amurka?


Bayan da aka kai hari kan tagwayen benayen World Trade Center a New York a 2001 (AFP)
Bayan da aka kai hari kan tagwayen benayen World Trade Center a New York a 2001 (AFP)

Mun yi waiwaye kan yadda aka kai wadannan hare-hare da suka sa Amurka ta mamaye Iraqi da Afghanistan domin yakar ayyukan  ta’addanci. 

A ranar 11 ga watan Satumbar 2001, ‘yan ta’adda suka kai wa Amurka hare-hare ta hanyar amfani da jiragen sama hudu, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a New York, Pennsylvania da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon.

Asabar 11 ga watan Satumbar 2021, shekara 20 cif kenan da aukuwar wannan hari.

Mun yi waiwaye kan yadda aka kai wadannan hare-hare da suka sa Amurka ta shiga a Iraqi da Afghanistan domin yakar ayyukan ta’addanci.

A yi karatu lafiya:

Daga karfe 7:59 na safe: Jiragen Amurka hudu suka tashi dauke da ‘yan ta’adda.

  • Jirgin American Airlines mai lamba 11 ya tashi daga Boston da misalin karfe 7:59 na safe.

  • Jirgin United Airlines mail amba 175 ya tashi daga Boston da misalign karfe 8:15 na safe

  • American Airline mail amba 77 ya tashi daga Washington da misalin karfe 8:20.

  • Sai wani jirgin United Airlines mai lamba 93 ya tashi daga Newark da misalin karfe 8:42

8:46 na safe – Jirgin farko mail amba 11, ya yi karo da daya daga cikin tagwayen benayen World Trade Center a New York.

8:59 na safe – Rundunar ‘yan sanda ta ba da umarni a fice daga tagwayen benayen biyu.

9:03 na safe – Jirgi na biyu da ‘yan ta’addan suka karkata akalarsa ya fadawa tagwayen benayen na biyu na World Trade Center.

9:05 na safe – Shugaban Amurka George W. Bush ya samu labarin harin yayin da yake ziyarar wata makarantar firaimare a Florida.

9:37 na safe – Jirgi na uku da ‘yan ta’addan suka sace, ya fada kan ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon.

9: 42 na safe – Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen a Amurka ta dakatar da tashin jiragen sama a daukacin kasar.

9: 45 na safe – Aka kwashe daukacin mutanen da ke Fadar gwamnati ta White House da ginin Majalisar Dokokin Amurka.

9:59 na safe – Ginin daya daga cikin tagwayen benaye na World Trade Center ya rushe.

10: 03 na safe – Jirgi na hudu ya fadi a wani fili a jihar Pennsylvania bayan da fasinjoji da matukan jirgin suka tunkari ‘yan ta’addan da suka karkata akalar jirgin.

10: 28 na safe – Ginin tagwayen benayen World Trade Center na biyu ya rushe.

11:02 na safe – Magajin Garin New York, Rudy Giuliani ya yi kira ga mazaunin unguwar Manhattan su fice daga yankin.

8:30 na dare – Shugaba Bush ya yi wa Amurkawa jawabi daga Fadar White House.

Kalaman da suka fara fita a bakin shugaba Bush: “Barkan ku da yamma. A yau, an kawo hari akan ‘yan uwanmu, da yanayin rayuwarmu da walwalarmu.”

XS
SM
MD
LG