Hukumar da ke binciken manyan laifuka ta FBI a Amurka, ta fitar da wasu sabbin takardun da ke dauke da bayanan sirri wadanda suka nuna irin taimakon da wasu ‘yan Saudiyya biyu da ke cikin maharan 9/11 suka samu gabanin kai hare-haren ta’addancin.
Takardun sun nuna yadda mutanen biyu suka rika tuntubar wasu ‘yan Saudiya mazauna Amurka kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.
Amma ba su bayyana wata hujja da ke nuna cewa manyan jami’an gwamnatin Saudiyya na da hanu a hare-haren ba.
Fitar da bayanan sirrin na zuwa ne yayin da Amurka ta gudanar da taruka don tunawa da hare-haren na 9/11 wadanda suka cika shekara 20 da aukuwa a ranar Asabar.
Wadannan bayanai sune na farko da aka fitar baina jama’a tun bayan da shugaba Joe Biden ya ba da umarnin a fitar da su bayan sun kwashe tsawon shekaru a boye.
Bayanan, wadanda suke kunshe a shafuka 16, na dauke da bitar tambayoyin da hukumar FBI ta yi wa wani mutum a 2015, wanda ya yi ta tuntubar ‘yan kasar Saudiyya da ke zaune a Amurka, wadanda su suka taimakawa maharan suka shiga Amurka gabanin kai munanan hare-haren.
A makon da ya gabata Biden ya ba ma’aikatar shari’a da sauran ma’aikatun gwamnati umarnin su saki bayanan.
Biden ya fuskanci matsin lamba daga iyalan wadanda hare-haren suka rutsa da su, kan a saki bayanan yayin da suka shigar da kara a New York inda suke zargin jami’an gwamnatin Saudiyya sun tallafawa maharan.
An yi ta zargin akwai hannun jami’an gwamnatin Saudiyya ne, tun bayan da aka sanar da cewa 15 daga cikin maharan 19 da suka kai hare-haren ‘yan kasar Saudiyya ne, sannan tsohon shugaban kungiyar Al Qaeda Osama Bin Laden, ya fito ne daga wani sanannen gida a kasar ta Saudiyya.
Ita dai gwamnatin Saudiyya ta sha nesanta kanta da hare-haren. Ofishin jakadancinta da ke Washington ya ce yana goyon bayan a fitar da duka cikakkun takardun bayanan sirri don a kawo karshen zargin da ake yi wa masarautar ta Saudiyya, wadanda ya ce “ba su da tushe.”
An saki wadannan bayanan sirri ne a daren Asabar bayan da aka tace su, sa’o’i bayan da Biden ya halarci wajen taron tunawa da hare-haren a New York, Pennsylvania, da kuma arewacin jihar Virginia.