Kamar yawancin biranen Amurka, jami’ai a Denver na Colorado na fadi-tashin magance matsalar bakin haure dake kwarara birnin. Fiye da bakin haure 1,500 ne suka isa a motocin bas tun ranar 9 ga Disamba, a cewar magajin garin Denver.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan al'ummar duniya ya kai biliyan 8, kuma fiye da rabin yawan al'ummar zuwa shekara ta 2050 za su fito ne daga kasashe takwas, biyar daga cikinsu a Afirka.
A Ghana kuma, babban abin da yafi jan hankalin mutane a shekarar 2022 shi ne tabarbarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa. A cikin shekarar ne aka samu hauhawar farashin kaya mafi kololuwa cikin sama da shekaru goma, sannan darajar kudin kasar ta fadi sosai.
A karshen shekarar 2022 ne shugaban Amurka Joe Biden ya karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka kimanin hamsin a Washington DC, inda ya sanar da tallafin dala biliyan 55 ga kasashen Afirka a fannoni da daban-daban cikin shekaru uku masu zuwa.
Mun yi waiwaye akan wasu lamura a shekarar 2022 a Najeriya kamar rashin tsaro rikicin Boko Haram wanda aka shafe shekaru ana fama da shi a Arewa maso gabashin kasar matsalar ‘yan fashin daji masu garkuwa da mutane, da sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, dama sauran matsaloli da aka samu.
Da zarar aka yi batun harkar ilimi a Najeriya a shekarar 2022, babban abin da ke zuwa ran mutane da dama shi ne yajin aikin sama da wata takwas da malaman jami’o’i suka yi. Yajin aikin dai ya nuna irin girman matsalolin da ake fama da su a bangaren ilimi a Najeriyar.
A Nijar kuma, masu sharhi kan al’amura sun ce duk da cewa an samu matsalolin tsaro a kasar a shekarar 2022, an samu gagarumar nasara wajen yaki da matsalar.
Wasu matasa masu fafutukar bunkasa al'adar karance-karance a Najeriya, sun shirya wani biki na mawallafa a birnin Jos, inda suka koka da yadda marubuta masu tasowa a yankin basa samun tallafi, abin da ke karya mu su kwarin gwiwa.
Ana ci gaba da zaman dar-dar tsakanin Fulani makiyaya da al'ummar Ejura a kudancin Ghana, yayin da majalisar gargajiya ta al’umar Ejura ta bai wa Fulani makiyaya a yankin umarnin ficewa.
Yayin da sauyin yanayi ke ci gaba da zama wani kalubale ga samar da abinci, wasu kasashen Afirka da suka dogara da shigo da hatsi daga waje, kamar Senegal, sun koma ga hatsi da suke iya samarwa a kasashensu.
Reverend Dr. John Bogna Bakeni, shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Jihar Borno ya yi kira ga Kiristoci a Najeriya da su ci gaba da koyi da halayen Yesu Almasihu, kamar hakuri, kulawa da kuma kaunar juna.
To anan Amurka ma, kamar a sauran wurare, Kiristoci a wani cocin ECWA a Maryland, sun yi bukukuwan Kirsimetin na bana ne da wakoki da raye-raye na tunawa da haihuwar Yesu Almasihu.
Domin Kari