A Jamhuriyyar Nijar ma, tsadar kayan masarufi a wannan lokaci, ta shafi irin shirye-shiryen da Kiristoci suke yin a bukukuwan Kirsimeti.
Bikin Kirsimeti ya sake zagayowa, wanda lokaci ne da Kiristoci a duniya suke bikin murnar Haihuwar Yesu Almasihu, sai dai hauhawan farashin kayan abinci da sutura, ya kawo babban cikas ga shirye-shiryen mutane na bikin.
Bisa al’ada, kowace sabuwar gwamnati a Amurka ta na bullo da manufofi a game da yadda huldarta da kasashen Afirka za ta kasance. Jami’an gwamnatin Joe Biden sun kyankyasa cewa wannan taro, zai bude wani sabon babin kawance tsakanin Amurkar da nahiyar.
Batun samar da tsaro wani muhimmin abu ne da kasashen Afirka ke son ganin Amurka ta kara kaimi wajen tunkararshi, ganin irin manyan kalubalen tsaro da nahiyar ke fama da su. Somaliya na cikin kasashen da matsalar tsaron ta fi shafa a Afirka.
A ranar Talata ne shugaba Joe Biden na Amurka ya karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka kimanin hamsin, a wajen babban taron da Amurka ta shirya da shugabannin Afirka a Washington.
Yayin halartar taron kolin Amurka da Afirka, shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum, ya yi hira da sashen Hausa, inda ya amsa tambayoyi kama daga tattalin arziki da tsaro da kiwon lafiya da dai sauran muhimman batutuwa.
Duk da cewa kasa da kashi hudu cikin dari kadai na hayakin dake gurbata muhalli Afirka ke samarwa, nahiyar ta na cikin wadanda suka fi fama da tasirin dumamar yanayi – kama daga ambaliyar ruwa zuwa karancin abinci. A wajen taron dai, an tabo batun yadda za a tunkari wannan lamari.
Yayin halartar taron kolin Amurka da Afirka, Khadijah Bazoum ta shaida wa muryar Amurka matakan da take dauka karkashin wani shirinta na “yaki da mugunyar tabi’ar tura mata barace-barace da sauran cin zarafi.”
Hukumar Zaben Najeriya INEC ta nuna rashin jin dadi game da karancin kasancewar mata a zaben dake karatowa, korafin da mata suka jima suna yi.
Masu jawabi a wurin taron lauyoyin sun yi tsokaci kan al’amura da suka hada da batun karba-karba, da batun addinin ‘yan Takara, da alkawuran ‘yan siyasa da kuma muradun jama’a.
A karkashin sabon tsarin, za a rika amfani da harshen asali na daliban firamare ne kadai wajen koyar da su daga shekarar farko zuwa shekara ta shida, yayin da za a sanya turancin Ingilishi daga matakin sakandare.
Kawo yanzu dai, Ghana ba ta fuskanci wata mummunar barazanar ta'addanci a 'yan shekarun nan ba, to amma duk da haka, kasar ta tashi tsaye don ganin ‘yan ta’adda basu yi mata bazata ba
Domin Kari