Renee Chuks, ƙwararriyar mai dafa abinci, ta fara gwaji tare da yin taliya daga rogo a cikin kicin ɗinta na Legas yayin da aka yi kullen ƙasa a Najeriya a 2020 sakamakon barkewar cutar coronavirus.
Shirin kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya leka kasuwar Mu da Lawal da ke garin Bauchi, bangaren ‘yan panteka don jin yadda harkokin kasuwar ke tafiya.
Shirin kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya leka fannin ‘yan kifi a kasuwar garin Ogbete da ke Enugu babban birnin jihar Enugu, inda wakilin Muryar Amurka Alphonsus Okoroigwe ya yi hira da ‘yan kasuwar.
A jihar Diffa ta Jamhuriyyar Nijar, manoman shinkafa fiye da duba-daya suka yi asarar shinkafar da suka noma a bana sakamakon bayyanar wasu tsuntsaye masu tarin yawa wadanda suka fito daga kasar Chadi mai makwbtaka da jihar. A cewar manoman, a tarihi ba su taba ganin irin wannan al’amarin ba.
Shirin kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya zaga kasuwar Sonita da wata kasuwar bisashe a birnin Maradi yayin da ake shirin bukukuwan babbar Sallar layya.
Farashin raguna kan kama ne daga N160,000 zuwa N170,000, wadanda kuma ake shigo da su daga sauran kasashe makwabta Najeriya kuma, sukan kai kimanin N600,000 zuwa N700,000.
Wakiliyar Muryar Amurka Hauwa Umar ta kai ziyara kasuwar Apo da ta Wuse a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya inda ta tattauna da wasu 'yan kasuwa.
A ranar 13 ga watan Yuli shirin karin kudin tikitin da aka yi zai fara aiki a daukacin jihar.
A cigaba da yunkurin nemo masalaha ga yawan rigingimu da ake samu tsakanin makiyaya da manoma a Najeriya, gwamnatin tarrayar kasar karkashin ma’aikatar noma da raya karkara ta kaddamar da wani sabon shiri da zai mai da hankali kan harkokin kiwo da inganta noma.
Shirin Kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya kai ziyara kasuwar Monday Market da ke cikin birnin Ilori a jihar Kwara.
Farashin man fetur ya haifar da kaso mafi girma na hauhawar farashin kayayyakin masarufi, hayar gidaje, farashin tikitin hawa jiragen sama da sauran abubuwa da dama.
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya bukaci kungiyar Tarayyar Turai da ta kara himma wajen taimaka wa kasashe masu tasowa don jure barnar da annobar cutar coronavirus tayi.
Domin Kari
No media source currently available