DIFFA, NIGER - Wannan al’amarin, ya zo a dai-dai lokacin da manoman shinkafar na jihar ta Diffa ke kokarin yanke shinkafar noman ranin da suka yi, kwatsam ba zato ba tsammani suka wayi gari da bayyanar wadannan tsuntsayen da suka mamaye illahirin gonakinsu.
Manoman dai sun yi amfani da hanyoyi da dama wajen korar wadannan tsuntsaye amma hakan bai samu ba sakamakon yawonsu, kamar yadda wasu manoman shinkafan suka shaida mana.
Ganin irin barnar da suka samu a bana manoman shinkafar na jihar Diffa sun fara tunanin irin matakan da zata dauka a nan gaba.
Mun yi kokarin jin ta bakin hukumomin dake kula da ayyukan noma a jihar ta Diffa game da wannan al’amarin, amma hakan bai samu ba.
A yanzu dai manoman shinkafar na jihar Diffa sun fara shirye-shiryen dasa shinkafar wannan damina, amma faruwar wannan al’amarin na tsuntsaye ya sa su cikin fargaba, musamman ma a wannan lokaci da ruwan Komadugu incin shi ya haura gibi sosai.