Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata ‘Yar Kasuwar Najeriya Ta Na Sarrafa Kayan Lambu Don Yin Taliya Mara Alkama

Wata ‘Yar Kasuwar Najeriya Ta Na Sarrafa Kayan Gona Don Yin Taliya Mara Alkama
Wata ‘Yar Kasuwar Najeriya Ta Na Sarrafa Kayan Gona Don Yin Taliya Mara Alkama

Renee Chuks, ƙwararriyar mai dafa abinci, ta fara gwaji tare da yin taliya daga rogo a cikin kicin ɗinta na Legas yayin da aka yi kullen ƙasa a Najeriya a 2020 sakamakon barkewar cutar coronavirus.

WASHINGTON, D.C. - Ta yi amfani da kayan gona da ake nomawa a cikin gida kamar rogo da ayaba wato plantain wajen samar da taliya da aka yi da hannu, ta kan kara ganye a ciki, wanda a yanzu take sayar da ita ta kamfaninta, Aldente Africa, wanda ta kafa shekaru biyu da suka gabata.Aldente Africa na daga cikin kamfanoni na farko da suka fara yin taliya mara alkama a Najeriya, in ji ta. Kasar na daya daga cikin manyan kasashen duniya da ke samar da rogo, kayan lambu mai arzikin ma'adanai da Vitamin C, shi ya sa kuma Chuks na ganin ya kamata Afirka ta kara yin amfani da amfanin gonakinta na cikin gida don taimakawa wajen inganta samar da abinci a nahiyar.

Wata ‘Yar Kasuwar Najeriya Ta Na Sarrafa Kayan Gona Don Yin Taliya Mara Alkama
Wata ‘Yar Kasuwar Najeriya Ta Na Sarrafa Kayan Gona Don Yin Taliya Mara Alkama

"Mun duba cikin gida don ganin, irin nau'in kayan da muke da su da muke ci a kowace rana. Rogo na ɗaya daga cikin manyan kayayyakinmu, manyan kayan aikinmu, don haka muka yi la'akari da cewa mu fara da wannan, idan za mu iya samun nasara mai kyau da rogo to. komai zai biyo baya," Chuks ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ne daga cibiyar kamfaninta da ke Legas.

Wata ‘Yar Kasuwar Najeriya Ta Na Sarrafa Kayan Gona Don Yin Taliya Mara Alkama
Wata ‘Yar Kasuwar Najeriya Ta Na Sarrafa Kayan Gona Don Yin Taliya Mara Alkama

Har ila yau, tana amfani da plantain da fonio, wani ɗan ƙaramin hatsi da ake nomawa a yammacin Afirka, wanda takan hada da wasu irin ganyaye da ganyayen gida, inda ya ke bai wa wasu taliya da ta yi launin kore ko ruwan hoda.

Kayayyakinta suna bazuwa a duniya sabode yanayin su na abinci na tushen shuka. Suna da cikakke tare da marufi ko fakiti masu kayatarwa da akan sayar akan dalar Amurka $2 zuwa $5 kowace fakitin taliya, suna ba da wadataccen bukata a yanzu.

Wata ‘Yar Kasuwar Najeriya Ta Na Sarrafa Kayan Gona Don Yin Taliya Mara Alkama
Wata ‘Yar Kasuwar Najeriya Ta Na Sarrafa Kayan Gona Don Yin Taliya Mara Alkama

Taliya na alkama ita ce abinci mai mahimmanci a Najeriya dalilin haka ya sa Chuks na ganin akwai sararin samun nasarar a kasuwa na kayayyakinta, wanda takan sayar akan intanet da kuma a cikin shaguna na kiwon lafiya. Kamfaninta kuma yana samar da giyar da aka yi daga shukin furen hibiscus da ganyayen girki.

-Reuters

XS
SM
MD
LG